31/01/2022
Albishirinku Al'ummar Jihar Zamfara Musamman Baki Masu Buƙatar Ingantaccen Masauki Domin Natsuwa Da Huta Gajiya.
Sabon tsarin masaukin baƙinmu ya bayyana ne a garin Gusau da samu Katafaren Masaukin Baƙinnan mai suna Zamzam Hotel.
A Zamzam Hotel mun tanadi ɗakuna manya da matsagaita da kuma ƙanana kamar:-
- Double room
- Luxury's suites
- Executive suites
- Diplomatic suites
- V.I.P
An inganta ɗakunan da makewayi "toilet" na zamani, da na'urar sanayay ɗaki wato AC, ga kuma talabijin mai ɗauke da tashoshi daban-daban, a sauƙaƙe ka kewaye duniya kana ɗakinka.
A ɓangaren gidan abincinmu kuwa tsafta itace jigonmu kuma itace mafi muhimmanci, abinci kuwa sai kalar wanda ranka yake so.
Mun tanadi ɗakin taro da zaku gudanar da taruka mabanbanta shagulgula da sauransu.
Idan kana a Zamzam Hotel baka da fargabar ɗaukewar wutar lantarki ko rashin ruwa tsawon awa 24 .
Idan haba-haba da baƙi ko samun natsuwa sune abun la'akari tabbas Zamzam Hotel mune a gaba sauran suna binmu a baya.
A ɓangaren abinda ya shafi tsaro kuwa to tabbas muna da ingantaccen tsaro a ilahirin zagaye da kewayen hotel ɗinmu.
Adireshinmu
Zamzam Hotel Yana Nan Behind King Fahad Hospital, Railway Crossing, Samaru, Gusau.
Daga Comr Haidar Hasheem Kano