21/08/2025
Kasancewarta Bazawara, an ɗaura auren ne bayan sallar Isha, da shedu mutum 5.
Bayan ƴan watanni kaɗan a gidan mijin sai taga tana shan wahala mutuƙa, daga ƙarshe mijin ya saketa.
Ta kai ƙara wajen Alƙali akan ƴan haƙƙoƙinta da ta ke bin mijin. Ko da zuwan mijin gaban Alƙali, sai ya ce, shi sam bai santa ba b***e ma ya taba aurenta.
Ta ce, Liman wane ne ya ɗaura auren kuma in aka kirawo shi ya san shedun da suke wurin. Aka kira Liman da Shedun nan 5 amma duk gaba ɗaya s**a musanta wannan auren, kuma s**a ce su sam ba su san komai ba....(Mijin ne ya basu cin hanci)!
Alƙali ya kalli matar nan ya ce, mijin ki yana kiwon Kare? Ta ce, Eh. Ya ce, in Kare ya yi miki hukunci za ki karba..? Ta ce, Eh! Akarmakallah.
Alƙali ya ce muje gidan. Idan karen ya yi haushi ko ya tasarmata ma'ana bai santa ba. Akasin haka na nuna cewa ya santa.
Ta shiga gida, Alƙali da ragowar jama'a na kallonta, Kare ya taso yazo jikinta (Saboda ta kasance tana ba shi abinci).
Alƙali ya ce, a yiwa shedun nan bulala 80 kuma a cire Liman daga limancin da yake.
Alƙali ya ce, TIR da al'ummar da karnukanta s**a fi mutanenta gaskiya...!!
✍️✍️ Auwal Sulaiman