06/12/2024
WANNE IRIN MUHIMMANCI KAKE BA WA RANAR JUMA'A???
Bismillahir-Rahmanir-Rahim....
Sheikh Muhammad Bin Salihul-Uthaimin (Rahimahullahu) yana cewa:
An ambaci Juma'a da suna Juma'a ne domin a cikinta ce Allah ya tattara al'amura da s**a faru na gani da ido (Kauniyya), da al'amuran da aka Shar'anta a addini (Shar'iyya) wanda bai tattara su a wasu ranaku ba.
Ranar Juma'a itace mafi girma da daraja daga dukkan ranakun mako, itace fiyayyarsu, Allah ya darjanta ta da tattara wasu abubuwa masu muhimmanci a cikinta:
- A ranar Juma'a ce aka kammala halittar Sammai da Qassai
- A ranar Juma'a ce aka halicci babanmu Annabi Adam (Alaihis Wasallam)
- A ranar Juma'a ce za'ayi tashin Alqiyamah kuma duk dai a ranar Juma'ar ce za'a tashi mutane daga Qaburbura
- A ranar Juma'a ce ake yin Sallar Juma'a mutane su taru a Massallaci guda daga wurare daban-daban
(TANBIHUL AFHAM:1/300)
Lallai yana da muhimmanci mu dinga girmama wannan rana domin rana ce da Allah (Subhanahu Wata'ala) ya keb'ance ta da abubuwa masu muhimmanci, haka ma Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) da Sahabbansa (RA) suna girmama wannan rana.
Saboda haka! Mu dinga koyi da Annabi da Sahabbai (SAW wa RA) domin samun tsira duniya da lahira.
Yana daga cikin Sunnar Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) yin wad'annan abubuwa a ranar Juma'a:
> Wanka na musamman domin Juma'a
> Sanya fararen tufafi
> Fesa turare mai Qamshi
> Zuwa Masallaci da wuri a samu ayi Nafilfili, karatun Qur'ani, sauraron Khuduba da Sallar Juma'ar
> Karanta Suratul Kahfi
> Yin Salati ga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam)
> Yawaita Du'a'I dss.
*************************************
Allah ya sada mu da dukkan alkhairan dake cikin wannan rana, ya kare mu daga dukkan sharrorin dake cikinta.
(Ameen)